BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Motar Buratai ta yi hatsari a Kaduna

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce motar babban hafsanta, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ta yi hatsari a jihar Kaduna da ke arewacin kasa.

Sanarwar da rundunar ta wallafa shafinta na Twitter wadda BBC ta kalato ta kara da cewa Laftanar Janar Buratai ba ya cikin motar lokacin da ta yi hatsari.

“Motar aiki ta babban hafsan rundunar sojin kasa ta yi hatsari a garin Jere a kan hanyarta ta zuwa Kaduna ranar 11 ga watan Nuwamban 2018 da misalin karfe 6.00 na yamma. Motar na cikin ayarin motoci lokacin da wata mota ta kauce daga kan hanyarta ta doki tasa,” in ji sanarwar.

Rundunar sojin ta ce mai tsaron lafiyar babban hafsan rundunar sojin ya samu raunuka inda aka dauke shi zuwa wani asibiti da ke kusa.

Daga bisani rundunar sojin ta ce an kai mai tsaron lafiyar Janar Buratai wani asibitin soji domin kula da lafiyarsa.

Kazalika an sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin inda aka soma bincike.

Sojojin sun ce binciken farko ya nuna cewa direban motar da ya bugi ta Laftanar Janar Buratai ya sha barasa gabanin ya soma tuki.

Leave a Reply