Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa, Uncategorized

Me ya sa aure ke saurin mutuwa yanzu?

Allah abin godiya! Yau ga shi mun shigo wani zamani – musamman a kasar Hausa da mutuwar aure ba ta zamo wani babban al’amari da za a damu da shi ba. Al’amura sun sauya ba kamar zamanin baya ba, wato zamanin da kafin ka ji aure ya mutu, sai da wani kwakkwaran dalili; wanda idan kowa ya ji, ba zai ji a ransa cewa aure ya mutu cikin ganganci ba.

Kwanci-tashi al’amura suna sauyawa ta yadda a kullum matsalolin kara ta’azzara suke yi, maimakon raguwa. Daga cikin matsalolin da suke kara ta’azzara, akwai wanda na ambata a sama: saki.

A dabi’ance, kamata ya yi a ce da zarar mutum ya yi aure sai ya samu wani irin sauyi cikin rayuwarsa ta yadda zai sauya daga rashin samun natsuwa zuwa ga samun natsuwa, daga rashin kwanciyar hankali zuwa ga kwanciyar hankali, daga kunci zuwa farin ciki. Amma kash! Abin yanzu kwata-kwata ba haka ba ne – ya jirkice.

Wani ma yakan ji da bai yi auren ba saboda tsabar bala’in da ya tarar a ciki. Za mu iya cewa daga mata da miji zuwa iyayensu (watakila da ’yan uwansu), kowa yana da nasa laifin wajen mutuwar aure. Wasu lokutan, iyaye kan zama silar mutuwar aure tun kafin auren ta hanyar tsauwala wa mijin da ’yarsu za ta aura wajen sayen kayan lefe da biyan kudin sadaki.

A daidai wannan gaba, Malam Muhsin Ibrahim, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma malami a Jami’ar Cologne, ya dan tabo mana yadda lamarin yake a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ya ce: “Wata ’yar uwata ta ban labarin wani aure da ta halatta. Angon sai da ya sayo akwatin lefe saiti 12.

A da, saiti 3 ake yi, sannan ya zamo 4, sannan 6, yanzu kuma 12! In da angon zai kawo kasa da haka, sai ’yan uwa da kawayen amaryar su koka, ba tare da la’akari da nauyin aljihunsa ba.” Malam Muhsin ya kara da jefo wasu ’yan tambayoyi:

Don Allah wace irin rayuwa muke son zaba wa kanmu ne? Me ya sa muke son tsauwala al’amura ga kawunanmu da gangan?” Ita wannan tsauwalar za ta kashe aure ne ta hanyar sanya miji ya rika ji a ransa kamar kudi ya zuba ya sayi matar.

Saboda haka, zai ji cewa duk abin da ya yi mata wanda ba daidai ba, babu bukatar ya ji ya yi mata kuskure. A haka sai zamantekawa ta rincabe. Sai kowa ya fara tauye wa kowa hakkinsa. Kafin ka ankara, aure ya mutu.

Kuma tsauwalar tana iya kawo rashin jituwa a tsakanin bangarorin biyu (wato bangaren amarya da na ango) bayan an yi aure. Hakan na saurin kashe aure ne domin shi mijin kullum zai rika kwana da tunanin cewa ba a tausaya masa ba lokacin da ya zo auren wannan yarinya.

Don haka, watakila, sai ya daina ganin kimar surukansa saboda ba su rangwanta masa ba. To ka ga ke nan tun daga nan an samu cikas. Wallahi tsauwalar ba ta da amfani. Saboda haka, don Allah, kowa – mace ko namiji, matashi da dattijo, mahaifi ko mahaifiya – ya yi kokari domin ganin ya bayar da gudunmawarsa wajen shawo kan wannan matsala domin ta shafi kowa

Muhammadu Sab’iu, Dalibi ne a Jami’ar Jihar Bauchi kuma za a iya samunsa a wayar tarho: 09078713542

Leave a Reply