BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa saboda abinci

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da ke Najeriya ta ce ta kama wani matashi da ake zargi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Gambo Isa, ya shaida wa BBC cewa matashin, dan shekara 25, ya yi amfani da tabarya wajen gudanar da aika-aikar da ta zama ajalin matar mai shekara 60.

Ya kuma jikatta mahaifinsa ta hanyar karya masa kafa.

A cewarsa matashin, wanda dalibi ne a wata jami’a da ke  Katsina, ya amince cewa yana shan miyagun kwayoyi.

Ya yi maganar cewa ba zai boye ba, gaskiya yana ta’amalli da miyagun kwayoyi kuma watakila da ta kan mahaifinsa ne zai fara saboda ya bi shi daki inda ya tarar yana sallah,” in ji SP Gambo Isah.

‘Yan sanda sun ce yanzu haka mahaifin matsahin yana asibiti yana jinya.

Bayanai sun ce mahaifiyar yaron ta dade ba ta gidan, kuma matar babanshi ce ta rike shi kuma ita ma tana da da, amma ya rasu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce matashin ya yi korafin cewa ya rika fuskantar rashin kulawa daga wurin kishiyar mahaifiyarsa musamman a kan abinci da wurin kwana.

A cewar SP Gambo Isa matashin ya rike wannan abu a cikin zuciyarsa

“Wannan abu da ya rike a zuciyarsa shi ne dalilin da ya sa ya fusata  har ya dauki wannan mugun mataki,” kamar yadda ya shaidawa BBC.

Kakakin ‘yan sandan ya ce nan gaba kadan za su gurfanar da matashin gaban kotu kan tuhumar kisan kai da ake yi masa

Leave a Reply