BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

‘Matan da ‘yan bindiga suka yi wa fyade sun haifa yara sama da 500,000’

Binciken wasu dattawan arewacin Najeriya na cewa ƴaƴan da aka haifa sakamakon fyaɗe da ‘yan fashin daji ke yi wa mata a yankunan Katsina zuwa Zamfara sun kai rabin miliyan.

Ɗaya daga cikin shugabannin dattawan na Katsina, Dr Bashir Kurfi ne ya shaida haka a wata hira da ya yi da BBC, kan matsalar tsaro a yankunan arewacin Najeriya, musamman katsina da Zamfara.

Dr Kurfi ya ce binciken da suka aiwatar cikin shekarun da aka kwashe ana yaƙi da ‘yan fashin daji, ya tabbatar musu da wadannan alkaluma sakamakon rahotanni da suka tattara daga kauyuka.

Ya ce mata da dama na kawo ƙorafinsu da kuma bayanai kan irin mutanen da suke yi musu fyade.

Yankunan Batsari da Dutsenma da Kankiya da Chiranci da su Funtua, Safana da dai sauransu duk ana samun irin wannan matsala a Katsina.

Ya ce a baya kafin matsalolin tsaro sai motoci 20 zuwa 50 su je Kano a rana ko daga Sokoto zuwa Kano ko ƙasashen makwabta, amma yanzu an daina, ‘yan kasuwa sun daina tafiya saboda haɗari da ke tattare da hakan.

Dr Kurfi ya ce girman matsalar tsaro ta wuce tunanin mutane, domin shiga gida ake yi kai-tsaye a ɗauki mata har da na aure.

A wasu kauyukan ma ‘yan bindiga waya suke yi wa magidanta su ce su kawo musu matansu da yaransu ko kanwa.

Ya ce baya ga kashe-kashen da ake yi ana cin zarafin mata, ana aikata fyaɗen gungun a kansu.

“Akwai macen da wallahi maza sama da 40 ne suka yi mata fyaɗe.

“Sai su kai hari kan babura sama da 100 da manyan makamai, ga kwayoyin da suke sha, abin tambaya, ta ina suke shigo da irin wadannan miyagun abubuwa.”

Leave a Reply