Kananan Labarai, Kano Ayau Hausa

Masu garkuwa sun sace jaririya, suna neman miliyan 100

Yau kwana 35 wannan jaririyar tana hannun masu garkuwa da mutane, ita yaririyar dai an haife ta da kwana 5 ne sai masu garkuwa da mutane suka shiga har cikin gida suka dauke ta a hannun mahaifiyarta, wani daga cikin masu garkuwar sai tausayi ya kama shi yace gaskiya a hada har da uwarta, inda nan take suka tasa keyar uwar jaririyar tana cikin jego kwana 5 da haihuwa haka suka tasa kiyar ta suka nufi daji da ita bayan sun hada mutane 5 a cikin gidan.

Wata majiya tace masu garkuwa da mutanen sun kira dangin mai jegon bayan yan kwanaki da cewa suna neman Naira Milyan 100 kafin su sako jaririn da Uwar jaririn.

Bisa haka ne Jaridar LEADERSHIP Hausa ta yi takakkiya ta ziyarci dangin mai jegon don yi masu jaje tare da jin ko wani hali ake ciki zuwa yanzu kwanaki 35.

Tuni suka ce har yanzu ba labarin sako wannan jaririyar da sauran wadanda aka yi garkuwar da su.

Don haka suke rokon al’uma da su taimaka musu da addu’o’i, kuma sun roki gwamnati ta taimaka masu kamar yadda aka taimakawa wasu da irin wannan jarabawar ta affaka masu.

Bincike ya tabbatar da cewa maharan sun kwashe a kalla mutane 6 a gida daya dukda jaririyar.

Wannan lamarin ya faru ne a wata unguwa da ake kira Sabuwar Abuja da ke a garin Giwa a jihar kaduna.

Leave a Reply