Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya, Laftana-Janar Tukur Buratai ya ce an samu shaidar da ke tabbatar da cewa akwai kungiyoyin mutane masu dauke da bindigogi, wadanda wadansu manyan mutane ’yan asalin Jihar Filato ke daukar nauyinsu da kuma daure masu gindi.
Janar Buratai ya bayyana haka ne a yayin da ake gudanar da jana’izar sojoji uku da aka kashe a yayin hautsinin da ya faru a ranar 6 ga watan Satumba a Karamar Hukumar Barikin Ladi. An gudanar da jana’izar ce a makabartar sojoji ta Madwell Khobe da ke Rukuba, Jos.
Janar Buratai, wanda Kwamandan Ayarin Samar da Zaman Lafiya na OPSH, Manjo Janar Augustine Agundu ya wakilta ya ce, “Akwai shaidar da ke tabbatar da cewa akwai wasu kungiyoyin ’yan bindiga, wadanda wadansu manyan mutane ke daukar nauyinsu tare da daure musu gindi wajen aiwatar da manyan laifuffuka da kashe-kashen mutane. Babu wata doka a tsarin mulki da ta ba wani mutum farin kaya ikon daukar bindiga, amma a nan Filato, al’amarin ya zama kamar dabi’a.”
Da yake nuna jimamin rasuwar Kofur Effiong Mbuotidem da Kofur Isah Ojaghale da Lansi-Kofur Kingsley Aloue, Hafsan Hafsoshin ya ce: “Kimar dan Adam ta zube a Filato. Jami’an Ayarin Samar da Zaman Lafiya, kamar sauran jami’an tsaro da aka kawo Filato, an kawo su ne bisa dokar aikinsu, domin su gudanar da aikinsu da tsarin mulki ya ba su, kuma suka yi rantuswar yi wa kasa hidima.”