Kano Ayau Hausa, Siyasa

Malam Shekerau ya janye daga takarar Sanata

Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP, ya koma Jam’iyyar PDP.

Malam Shekarau ya bayyana hakan ne a gidansa, a lokacin da dan takarar Shugaban Kasa a PDP, Alhaji Atiku Abubakar da sauran jagororin PDP suka je gidansa domin karbarsa zuwa PDP.

A cewarsa, ya fice daga NNPP, sannan ya rubutawa INEC cewa ya janye daga takarar Sanatan Kano ta Tsakiya da zai yi.

Wannan shi ne karo na biyu da Shekarau ya canja jam’iyya a bana.

 

Leave a Reply