Kano Ayau Hausa, Siyasa

Majalisar Shura ta gindaya sharuda biyar kafin Shekarau ya koma PDP

Majalisar ta Shura ta gidan siyasar Malam Ibrahim Shekarau, ta gindaya sharudda guda 5 na sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar PDP.

Sharuɗɗan sun kasance wani ɓangare na rahoton Shura ɗin da za ta gabatar wa Shekarau a yau Asabar .

Jaridar DAILY NIGERIAN ce ta fallasa shirin Malam Shekarau na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP, duk da samun tikitin takarar sanata da ya yi a jam’iyar.

Lokacin da Shekarau ya bayyana batun tattaunawar da yake yi da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma tayin da aka yi masa, a gaban ƴan kwamitin Shura, rahotannin sun bayyana cewa sai da a ka samu rarrabuwar kai a majalisar.

Yayin da wasu suka bayyana ra’ayinsu na sauya sheka zuwa PDP, wasu kuma sun goyi bayan matakin na Malam Shekarau saboda “NNPP ta kasa baiwa mutanen Mallam gurbin takara a jam’iyyar.

Wata majiya mai tushe da ta so a sakaya sunanta ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa a wani ɓangare na tayin da aka yi na neman Malam Shekarau, Atiku Abubakar ya yi alkawarin nada shi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya ko kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa idan ya ci zaɓen 2023.

Majiyar ta ƙara da cewa Shekarau ne zai jagoranci yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma, tare da bayar da umarnin kai wa shugabannin addini da na gargajiya goyon baya, duba da cewa Malam yana da kyakkyawar alaka da malamai, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.

A makon da ya gabata ne aka kafa wani kwamiti mai mambobi 21 don yin nazari kan wannan shawara tare da bayar da rahoto kan ci gaban da aka samu.

Sai dai wani babban na hannun daman Malam Shekarau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar cewa ba Sanatan ne ya zo da bukatar sauya sheka ba, wasu manyan Arewa ne.

A cewar majiyar, batutuwa biyu – matsin lamba daga manyan Arewa da abokansa ya sanya Malam Shekarau ya koma PDP.

“Mallam ya damu musamman saboda gunaguni cikin gida game da yadda yake son kansa ba tare da nemawa mutanensa mukamai ba. Yayin da Malam yake kokarin shawo kan rikicin cikin gida, sai dattawan Arewa suka fara kiransa da ya zo ya hada kai da Atiku,” inji majiyar.

Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun Malam Shekarau, Sule Ya’u Sule ba, wanda tun da farko ya shaida wa manema labarai cewa za a yanke shawara a cikin makon nan.

Leave a Reply