Kano Ayau Hausa, Kiwon Lafia

Mai sa mutane azumin mutuwa a Kenya, ya mutu

Daya daga cikin mutane 30 da ke hannun ‘yan sanda bisa zargin kasancewa mambobin wata ƙungiyar asiri da ke horo da yunwa a Kenya, ya mutu.

Joseph Juma Buyuka – tare da wasu a cikin waɗanda ake zargi – sun yi yajin cin abinci a farkon wannan wata don nuna adawa game da kama shin da aka yi.

An garzaya da shi zuwa asibiti a garin Malindi da ke kudu maso gabashin Kenya, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

“Muna zargin ya mutu ne sanadin larurorin ƙauracewa abinci. Za mu iya jira a yi gwajin gawa don gano ainihin musabbabin mutuwar,” wani babban mai shigar da ƙara ya faɗa wa wata kotu a Mombasa, babban garin gabar tekun Kenya, ” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Har yanzu, babu ɗaya a cikin wadanda ake zargi, waɗanda suka haɗar da shugaban ƙungiyar asiri, Paul Nthenge Mackenzie da aka gurfanar a kotu, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da bincike.

An yi imanin cewa faston da sauran waɗanda ake zargin sun ingiza mambobin Cocin Good News International wajen kashe kansu da yunwa.

Tun a watan Afrilu, aka tono gawawwakin mutane 336 daga kaburbura marasa zurfi a wani dajin da ke nesa.

Fiye da wasu 600 ne suka bace.

An kwantar da mutum biyu da ake tsare da su saboda su ma suna yajin cin abinci, a asibiti cikin mawuyacin hali.

Kotun za ta yanke hukunci a ranar Talata mai zuwa ko Mista Mackenzie zai ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan sanda tsawon kwana 60 ko a’a.

Leave a Reply