Kano Ayau Hausa, Siyasa

Mai ba Ganduje shawara, Mai rigar fata ya Koma NNPP

A jiya Lahadi 10 ga watan Afrilun 2022 ne Mai bawa gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje shawara ta musamman akan harkokin matasa da sana’o’in dogaro da kai, Hon. Abdulmajid Isa (Mai Rigar Fata) ya fice daga jami’yyar APC mai mulki ya koma jami’yyar NNPP ta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hon. Abdulmajid yana ɗaya daga cikin makusanta gwamna da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alh. Abdullahi Abbas domin ƙaramar hukumar su ɗaya ta Gwale, kuma rahoton da muka samu daga wata majiya mai tushe ta ce tabbas ya fice daga APC ya koma NNPP bisa raɗin kansa da shawarwari ƴan siyasa gidan sa saboda wasu dalilai da ba a bayyana mana su ba, Sai dai sun ce dama can akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Kwankwaso da Mai Rigar Fata.
Kazalika, Tun farko dai mashawarci na musammna ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso akan kafafen yaɗa labarai na zamani, wato Saifullahi Hassan shi ne ya wallafa hotunan ficewar Abdulmajid din a shafinsa na Facebook tare da Kwankwaso inda yake sanya masa jar hula alamar ya karɓi shahadar Kwankwasiyya a gidan sa da ke babban birnin tarayyar Abuja.

Leave a Reply