WASANNI

Magoya bayan Madrid sun fara korafi

Magoya bayan kulob din Real Madrid da ke Sifen sun fara korafi musamman ganin yadda kulob din ya yi wasanni uku a jere ba tare da ya samu nasara ba.

Rabon da kulob din ya samu kansa a cikin irin wannan hali tun kimanin shekara 10 da suka gabata, kamar yadda jaridar Balon dor da ake wallafawa a Sifen ta kalato.

Rahotannin da suka fito daga Madrid sun nuna yadda magoya bayan kulob din suka harzuka a ranar Talatar da ta wuce, jim kadan bayan kulob din CSKA Mosko ya lallasa na Madrid da ci 1 mai ban haushi a gasar Zakarun Kulob na Turai.

Duk da cewa Madrid ce ta fi rike kwallo a wasan, inda take da kashi 73 kuma ta kai hare-hare har sau 26, hakan bai sa ta fanshe cin da CSKA Mosko ta yi mata ba.

Yanzu dai Real Madrid ta yi wasanni uku ke nan a jere ba tare da ta samu nasara ba, wanda hakan ke nuna akwai matsala a kakar wasa ta bana. Tun bayan da Cristiano Ronaldo ya canja sheka daga Madrid zuwa kulob din Jubentus na Italiya a kakar wasa ta bana ne, kulob din yake tangal-tangal saboda rashin kwararrun ’yan wasa.

Masana harkar kwallo sun yi hasashen da wuya Real Madrid ta iya lashe wani kofi a kakar wasa ta bana idan aka yi la’akari da karin maganar da Hausawa kan yi na “Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake ganewa.”

Leave a Reply