Kano Ayau Hausa, Labarai

Limamin Juma’a ya ajiye limanci saboda takarar kansila a Katsina

Wani Limamin Juma’a, Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA a Jihar Katsina ya ajiye muƙamin limancin saboda zai tsaya takara.

A wasiƙar ajiye limancin da ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.

Wani ɓangare na wasiƙar, wacce Daily Nigerian Hausa ta ruwaito, ya ce” Ni Muhammad Hashim (Liman) na aje muƙami na na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA sabo da tsayawa takara da zan yi.

“Ina fatan Allah SWT Ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, Ya yafe mana kusa-kuren mu Amin.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ƴan kwamitin masallacin da ma al’umma baki ɗaya.

Leave a Reply