Kano Ayau Hausa, Siyasa

Kwamitin yakin zaben Atiku ya nemi a dakatar da sanar da sakamako

Kwamitin yakin neman zaɓen Atiku Abubakar ya yi fatali da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya da ake ci gaba da fitarwa, inda ya yi kira da a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar wanda ya samu sa hannun mai magana da yawunsa, dakta Daniel Bwala, ta ce ɗaya daga cikin zaɓin da ya rage wa INEC shi ne ta dakatar da karɓa da kuma sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da take yi.

Daniel Bwala ya ce dakatar da karɓar sakamakon ya zama tilas don shawo kan matsaloli da jam’iyyu suka yi korafi a kai dangane da rashin amfani da na’urar BVAS da kuma kasa tura sakamakon zaɓen zuwa shafin INEC kamar yadda BBC ta ruwaito.

Ya ce abin da ya kamata INEC ta yi a yanzu shi ne sanya sabon ranar gudanar da zaɓe a wuraren da aka fuskanci matsalar, da kuma tabbatar da cewa an aika sakamakon zuwa shafin yanar gizo na hukumar zaɓe.

Sanarwar kwamitin ta ƙara da cewa a soke dukkan sakamakon zaɓen da aka sanar har sai lokacin da aka aika sakamakon da aka tattara a rumfunan zaɓe zuwa shafin INEC.

Kwamitin ya kuma ce INEC ta fito ta yi wa ‘yan ƙasa jawabi kan sahihancin zaɓe da ta gudanar don samun ƙwarin gwiwa ga al’ummar ƙasar da ma na ƙasashen waje.

Leave a Reply