A wata sanarwa da kwamishinan shari’a na jihar Kano ya fitar.
Kwamishinan ya yi nuni da cewa, kwamishinan ‘yan sandan ya kasa bin umarnin da Gwamna ya bayar a matsayinsa na babban jami’in tsaro, yana mai cewa yana aiki ne da umarnin Wasu daga samaYa ce, “Ai tilas ne in yi tambaya: wane ne ke kwace ikon Babban Kwamanda.
Domin wasu mutane na yin watsi da umarni ga shugabannin tsaro a jihar ta yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar ba tare da wani shawara da babban jami’in tsaro na jihar ba ko amincewar kwamitin tsaro na jihar ya bayar da umarnin hana Eid-el-Kabir bukukuwa a jihar Kano.
“Ta yaya wani daban ba Gwamna ba zai hana bukukuwan Sallah a Kano? kuma yaushe ne aka kwace mukamin Babban Jami’in Tsaro na Jihar da zai ga irin wannan haramcin a kafafen sadarwa na zamani?
Wanene ke ingiza Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya kwace ikon Gwamna? “Yana da mahimmanci a nanata cewa Kwamishinan ‘yan sanda ya kasance mai tsayin daka wajen kin bin halalcin umarnin Gwamna a matsayinsa na Babban Jami’in Tsaro, yana fakewa da umarni daga sama.