Kano Ayau Hausa, Latest News

Kungiyar ta’addanci ta fara jan hankalin matasan Kano

Kungiyar ta’addanci ta Ansaru, wadda sashen Boko Haram ce ta fara jan hankalin matasa a Jihar Kano.

Jaridar Sahelian Times ta ruwaito cewa kungiyar tana jan hankalin matasa ne ta hanyar ba su kudi a wajajejn karatu da sauransu.

Wani matashi mai kimanin shekara 27 da yanzu yake karatu a jami’a ya bayyana wa Sahelin Times cewa bai san inda suka hadu da wani mutumi ba, amma yana tunanin sun hadu ne a wajen karatu.

“Ban san akidarsa ba, sai kawai DSS suka zo suka kama ni. Amma bayan bincike ne aka sake ni bayan an gano muna gaisawa ne kawai, amma bai ja hankali ba.”

Akwai kuma wani matashi ma da har ya riga ya tafi atisaye a wajen kungiyar ta’addancin, kafin daga baya ya gudo bayan ya ga suna bautar wani abu daban.

Haka kuma akwai matashi da yanzu haka yake hannun jami’an tsaro bayan an kama shi da alaka da kungiyar ta’addancin.

 

Leave a Reply