BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kungiya Ta Bukaci A Dawo da Tsarin Masarauta 1 a Kano

Kungiyar KACDA, wacce ke rajin kare martabar al’adun jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar, da ya rushe tsarin masarautu biyar Kungiyar ta nemi da a dawo da tsarin sarki ɗaya tilo a jihar domin dawo da martaba da kwarjinin masarautar Kano a idon duniya Shugaban kungiyar, A.G. Shittu ya koka kan yadda aka samu rarrabuwar kawunan al’umma da lalacewar al’adu saboda raba masarautun Jihar Kano – Kungiyar kare martabar al’adun gargajiya ta Kano (KACDA) ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta rushe tsarin masarautu biyar a jihar.

Kungiyar wacce ta aika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf wata wasiƙa kan wannan bukatar ta ce rabuwar masarautun ta rage daraja da martabar babbar masarautar Kano. Wasikar wacce ke dauke da sa hannun shugaban kunyar KACDA na jihar, A.G. Shittu na magana ne akan masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye da aƙa kirkira a baya. A.G. Shittu ya ce raba masarautar da aka yi gida biyar ya jawo rarrabuwar kawuna da lalacewar al’adun dauri wadanda aka san masarautar Kano da su. An rage wa masarautar Kano kwarjini a idon duniya A zantawarsa da Legit Hausa, Shittu ya ce: “Misalin hawan daba da ake yi a bikin Sallah, kafin rabuwar masarautun, dukkan kananan hukumomi 44 na haduwa a masarauta daya ne, amma yanzu an raba kawunan mutane.

“Daraja da martabar masarautar Kano ta yi ƙasa, maimakon sarki guda ɗaya mai cikakken iko, yanzu sarakuna biyar ne, don haka ita uwar masarautar an rage mata kwarjini a idon duniya” Shugaban kungiyar ya ce sun aika wa gwamnan wasikar don ankarar da shi illar da take tattare da rabuwar masarautun da kuma ba shi shawarar hanyar dawo da martabar Kano.

Ya ce: “Ya zama wajibi gwamnatin Kano da majalisar jihar Kano su yi fatali da waccan doka da ta kafa masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye ma damar ana son dawo da martabar masarautar Kano.

Wa za a nada sabon Sarkin Kano? Ko da aka tambaye shi akan wanda ya ke ganin zai zama sabon sarki idan an hade masarautun waje daya, Shittu ya ce: “Dukkannin wadanda suke da sha’awar zama kan kujerar, za su aika da bukatar hakan, muna da yakinin gwamnati za ta zabi wanda ya fi cancanta ya zama Sarki. Hausa.lagit.ng

Leave a Reply