Kano Ayau Hausa, Labarai

Ku saki kudi ko in kore ku-Zulum ga bankuna

Gwamnan Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi bankunan kasuwanci a jihar cewa gwamnatinsa za ta ƙwace lasisin filin duk bankin da ya gaza saka sabbin takardun naira a na’urorin cire kuɗi na ATM.

Gwamnan ya yi gargaɗin ne ranar Juma’a a birnin Maiduguri lokacin da ya kai ziyara don gane wa idonsa irin dogwayen layuka da wahalar da jama’a ke fuskanta na ƙarancin sabbin takardun kuɗin.

“Duk bankin da ba shi da niyyar cika ATM ɗinsa da sababbin takardun kuɗi don sauƙaƙa wa al’umma wahalhalu, za mu ƙwace filin gininsa nan take,” in ji gwamnan cikin wata sanarwa da kakakinsa Isa Gusau ya fitar kamar yadda BBC ta ruwaito.

Sanarwar ta ce ran Gwamna Zulum ya ɓaci ne lokacin da ya tarar da wani dogon layin cirar kuɗi, inda ATM ɗaya ne kacal yake aiki cikin 10 da ke wurin.

“Kamar yadda kuke gani, talakawa ne kawai a kan layi…An ce wasu tun ƙarfe 3:00 na dare suke a nan, wasu ma ba su ci komai ba. Sababbin kuɗin da tsofaffin duka babu, wanda hakan ke shafar harkokin kasuwanci tare da ƙuntata wa mutane,” a cewar Zulum.

Gwamnan ya ƙara da cewa lokacin da ya je Ƙaramar Hukumar Gubio ya tarar cewa babu naira N100,000 a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya na tsofaffi ko sababbin kuɗin.

Leave a Reply