FITATTUN MATA, Kano Ayau Hausa

Kotu ta tura Sanata Ekweremadu da matarsa gidan yari

Wata kotu a Birtaniya ta daure Sanata Eke Ekweremadu a gidan yari na shekara 10 da wata 6.

Haka kuma ta daure matarsa, Beatrice Ekweremadu shekara 6, sannnan ta daure likitansu, Dokta Obinna Obeta na shekara 10.

An yanke musu wannan hukuncin ne bisa samunsu da laifin safarar sassan jikin Dan Adam.

Idan ba a manta ba, Sanata Ike ya dauki wani matashi zuwa Landan da nufin matashin zai ba diyarsa kodarsa domin nata ya samu matsala.

Sai dai matashin bayan isansa Birtaniya ya ce shi bai san kodarsa zai ba diyar Sanatan ba, shi kuma Sanata Ike ya ce lallai da wajewa suka yi cewa za su kai matashin wanda dan talakawa ne Landan ne domin ya ba diyarsu din kodarsa.

Karyatawar da matashin ya yi ne ta sa kotu ta yanke wa Sanata Ike da matarsa da likitansu wannan hukunci.

Sai dai akwai damar daukaka kara idan masu laifin ba su gamsu ba.

Leave a Reply