GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Kotu ta hana belin jami’in Binance

Wata babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami’in kamfanin kuɗin kirifto na Binance, Tigran Gambaryan da hukumomin ƙasar ke tsare da shi.

Yayin da yake gabatar da hukuncin, mai shari’a Emeka Nwite ya ce ya yi nazarin takardar neman belin da aka gabatar masa, sai dai ya ce akwai yiwar mista Gambaryan zai iya tserewa idan aka bayar da belinsa.

An gurfanar da kamfanin tare da shugabanninsa gaban kotun ne bisa zarge-zarge biyar masu alaƙa da ɓarnatar da kuɗi.

Leave a Reply