Labarai

Kotu ta dakatar da majalisa daga binciken bidiyon Ganduje

Wata kotun jihar Kano ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga binciken da take yi a kan zargin da ake yi wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karbar hanci da aka fallasa a bidiyo.

Alkalin kotun A. T Badamasi, ya umarci kwamitin bincike da majalisar jihar ta kafa, da ta dagatar da binciken da ake akan bidiyon Gwamna Ganduje.

Wata qungiyar lauyoyi wanda shugaban kungiyar Barista Muhammad Zubair yake jagoranta ya yi zargin cewa majalisar dokokin jihar Kano ba ta da hurumin gudanar da bincike a kan Gwamna Ganduje kasancewar yana da rigar-kariya.

Leave a Reply