Kano Ayau Hausa, Labarai

Kotu ta ba DSS damar ci gaba da tsare Mamu na kwana 60

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Talata ta baiwa Hukumar Ƴan Sandan Farin Kaya, DSS damar su cigaba da riƙe Tukur Mamu, mai sasanta wa tsakanin ƴan ta’adda da iyalan wadandaa akai garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja-Kaduna, har tsawon kwanaki 60.
Mai Shari’a Nkeonye Maha ya bada umarnin ne biyo bayan lauyan hukumar tsaro ta farinkaya ya nemi da a kara musu lokaci don cigaba da binkice akan Tukur.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa ‘yan sandan Masar sun kama Tukur Mamu tare da iyalansa a ranar 6 ga watan Satumba, ya yin da yake kan hanyar sa ta zuwa Saudiyya domin yin Umara, daga karshe suka dawo dasu gida Najeriya, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta kalato.
A ranar Lahadin ta gaba ta jami’an na hukumar ta DSS suka jawa ‘yan Najeiya kunne kan tufar albarkacin bakin su akan kama Tukur Mamu.
Daga cikin abubuwan da DSS ta ce ta gano a gidan Mamu akwai Dala 150 da, da Fam 20 da Rufin Indiya 1,530 da Riyal 1 da Dirhami 70 da Naira miliyan da dubu dari biyar da shida da kakin sojojin kasa guda takwas da na sojojin ruwa 16 da lasisin rike bindiga da sauransu.

Leave a Reply