Kano Ayau Hausa, Labarai

Kotu a Kano ta daure matashin da ya ce babu Allah shekara 24

Kotu ta ɗaure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan laifin ɓatanci ga addinin Islama.

An yanke masa hukunci ne kan laifuka 18 da aka zarge shi ciki har da amsa laifin aikata sabo a gaban kotu.

Sai dai ya shaida wa kotun cewa lokacin da ya yi rubutu bai san cewar saƙon zai iya haifar da tashin hankali ba, sannan kuma hakan ya zama darasi a gare shi, nan gaba.

An kama Mubarak Bala, shugaban kungiyar wanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook.

Sakon da ya wallafa ya fusata al’ummar musulmi a Najeriya, kamar yadda muka kalato daga BBC.

Leave a Reply