Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta ce kaso uku cikin hudu na daliban da suka zana jarabawar kammala sakandare a bana sun ci darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
A cewar hukumar, daga cikin dalibai 1,601,047 da suka rubuta jarabawar, guda 1,222,505 ne suka samu nasarar cin darussa biyar.
Haka kuma ta ce dalibai miliyan 1,409,529 sun sami nasara a darussa biyar, wasu da Lissafi wasu kuma da Turanci kadai.
Hukumar ta bakin shugabanta na Najeriya, Mista Patrick E. A. Areghan, a cikin wata sanarwa da yammacin Litinin ta ce jimillar dalibai 1,607,981 ne dai suka yi rajistar jarabawar daga cibiyoyi 20,222 da ke fadin kasar nan.
Sai dai WAEC ta ce dalibai miliyan 1,601,047 ne suka sami rubuta jarabawar daga cikin wancan adadin kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Haka kuma, Areghan ya ce daga cikin wadanda suka yi jarabawar, sakamakon dalibai 1,437,629 ne hukumar ta saki, yayin da na ragowar 163,418 zai fita nan da mako guda.
Wannan dai na nuna kashi 76.36 cikin 100 na daliban ne suka sami nasarar cin darussa biyar, ciki har da Lissafi da Turanci.
Haka zalika kiyasin hukumar na nuna kaso 37 daga wadanda suka sami nasarar maza ne, yayin da mata ke da kaso 39.