Rundunar yan sandan jihar Kano ta gurfanar da ɗan Chinan da ake zargi da kisan Ummukulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita a ranar Laraba, gaban wata kotun majistire.
Ana zargin Mista Geng Quanrong da kisan matashiyar, lamarin da ya ci karo da sashe na 221 na kundin laifuka na jihar Kano, a cewar kotun.
BBC Hausa ta ruwaito kotun a ta aike da dan kasar Chinan kurkuku.
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare, inda Geng Quanrong, mai shekara 47, ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.
Kisan Ummita ya tada hankalin al’umma ‘r jihar Kano da dama har da Najeriya, abinda ya jawo mutane suka dinga neman ayi mata adalci a kafafen sada zumunta.