BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kasar Kenya na fama da karancin kwaroron roba

Kungiyoyin fararen hula a Kenya na kokawa kan matsanancin ƙarancin kwarororn roba da ake rabawa kyauta a ƙasar.

Akan shigar da kwaroron ne daga ƙasashen waje domin rabawa kyauta ga mabuƙata, sai dai masu samar da kwaroron sun daina kai wa Kenya saboda harajin da aka tsananta a kansa.

Masu hanƙoro na son ganin an cire haraji a kan shigo da kwaroron, kasancewar hakan zai daƙile yaɗuwar cuta mai karya garkuwar jiki (HIV).

Daily Nigerian Hausa ta ruwaito daga BBC cewa ana buƙatar kwaroron roba miliyan 455 kowace shekara a ƙasar ta Kenya, sai dai gwamnati tana iya samar da miliyan 150 ne kacal.

Ana ƙarfafa wa mutane gwiwa wajen amfani da kwaroron roba domin kare kansu daga cutuka kamar HIV, da kuma cutar sanyi.

Sai dai a tsawon shekara biyu da suka gabata an rinƙa fuskantar ƙarancin kwaroron a asibitocin gwamnati da ke faɗin ƙasar.

A yanzu ana samun kwalin kwaroron a kan farashin da ya kai dalar Amurka ɗaya, abin da ya fi ƙarfin mutane da dama.

Tun a shekarar 2020 ne dai ake samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar HIV a ƙasar ta Kenya.

Leave a Reply