Kano Ayau Hausa, Siyasa

Kamfe: Sabuwar rikici ta kunno kai a APC

2023: Sabon rikici ya kunno kai a APC bayan fitar da sunayen ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓe

Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyya mai mulki ta APC, biyo bayan sakin sunayen majalisar yakin neman zaben shugaban kasa, mai ɗauke da mambobi 422.

Kwamitin Ƙoli na APC, NWC, karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu ya rubuta wasiƙa zuwa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu, inda ya zarge shi (Tinubu) da yin gaban kansa wajen fitar da sunayen.

A cikin wasikar da ya fitar a safiyar yau Alhamis, Adamu ya zargi Tinubu da saɓa yarjejeniyar da ya ƙulla da NWC dangane da batun kafa kwamitin yakin neman zaɓen.

An dakatar da batun kafa majalisar saboda an ce NWC ta kafa wani kwamiti mai mutane uku don yin aiki hannu da hannu da tawagar Tinubu.

Mambobin NWC sun kasance Sakatariyar Tsare-tsare ta Kasa, Mai Ba da Shawara Kan Shari’a da Mataimakiyar Shugaban Mata da aka kafa domin daidaita jerin sunayen ‘yan majalisar da tawagar Tinubu.

“Shawarwari na tawagar NWC shine a samu Sanata Adamu a matsayin mataimakin shugaban majalisar; Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa (Arewa), Sanata Abubakar Kyari a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Yankin (Arewa) da takwaransa na Kudu, Hon. Emma Eneukwu a matsayin Mataimakin Shugaban Gudanarwa na Yanki (Kudu), kamar yadda muka kalato daga fassarar Daily Nigerian Hausa.

Bukatar ta kuma haɗa da samun Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sen. Iyiola Omisore a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar; babban sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Sulaiman Argungu a matsayin mataimakin darakta Janar (Kungiyoyi); Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (South South), Hon. Victor Giadom a matsayin mataimakin kodinetan yakin neman zaben shiyyar kudu maso kudu da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (kudu maso yamma) a matsayin mataimakin kodinetan yakin neman zaben shiyyar.

“Ina mai isar da ra’ayi na gaba ɗaya na NWC game da fitar da jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen da aka yi a lokacin da bai dace ba kuma bamu ji daɗin hakan ba.

“Wannan mataki ya ɓata wa wasu rai maimakon faranta wa ƴan jam’iyya wanda janyewarsu zai tabbatar wa NWC na mutuntawa da martaba wa gare ka da kuma jam’iyyar mu,”

Leave a Reply