Kano Ayau Hausa, RAHOTANNI

Iran na cigaba da jefa rokoki a Isra’ila

Dakarun sojin Isra’ila sun ce sun yi haɗaka da wasu ƙasashe wajen daƙile gomman harin makami mai linzami da Iran ta kai mata.

Wannan bayani martani ne ga harin makami mai linzami ta sama da Iran ta kaddamar kan Isra’ila.

Karon farko kenan da ƙasashen biyu za su yi amfani da ƙarfin soji a kan juna, bayan shafe shekaru ana nuna yatsa da kuma yarfe ga juna.

Tuni dai firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya kira taron majalisar ƙoli ta yaƙin ƙasar domin tantance mataki na gaba.

Dama dai Iran ta sha alwashin kai harin ramuwa kan Isra’ilar, tun bayan wani hari da aka kai ofishin jakadancin ta da ke Syria, a ranar ɗaya ga watan Afrilu.

Dama dai Iran ta sha alwashin kai harin ramuwa kan Isra’ilar, tun bayan wani hari da aka kai ofishin jakadancin ta da ke Syria, a ranar ɗaya ga watan Afrilu.

Iran ta zargi Isra’ila da kai harin, wanda ya kashe wani babban kwamandan rundunar juyin-juya hali, sai dai Isra’ila ta ce ba ta da hannu a harin.

A wani jawabi, kakakin rundunar tsaron Isra’ila, Rear Admiral Daniel Hagari ya ce dakarunsu da gamayyar ƙawayen su sun yi nasarar daƙile ɗaruruwan makamai masu linzami da Iran ta harbo.

Ya ce an samu wajen da wasu makaman suka faɗa, a cikin Isra’ila, amma ba su kashe kowa ba.

Jami’an gwamnatin Amurka da na Birtaniya ma duk sun tabbatar da cewa dakarun ƙasashensu sun taimaka wajen daƙile harin na sararin samaniya.

Shugaba Biden na Amurka ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyar G7 a yau Lahadi domin tattauna matakan da ya kamata a ɗauka kan batun.

Leave a Reply