BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ina farin ciki mun daidaita da Shagari – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana godiya ga Allah cewa dangantakar da ke tsakaninsa da marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari tsohon shugaban kasar mai cikakken iko na farko ta gyaru.

Ya ce duk da bambancin ra’ayi a kan wasu batutuwa, amma sun yi nasarar gyara alakar da ke tsakaninsu.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar don bayyana alhininsa game da rasuwar Shehu Shagari kamar yadda BBC ta wallafa.

Ya bayyana Shagari a matsayin kamilin mutum dan kishin kasa da ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannoni da dama wajen ciyar da kasa gaba.

Muhammadu Buhari ne dai ya jagoranci kifar da gwamnatin marigayi Shehu Shagari lokacin yana babban hafsan soja a 1983.

Sai dai a cikin sanarwar, Buhari ya ce mutuwar Shehu Shagari, wani babban rashi ne ga Najeriya.

A cewarsa, Najeriya ta yi asarar wata gada wadda ke hada dangantaka tsakanin tsoffin ‘yan kishin kasa da suka yi fafutukar kwato ‘yancin kai da kuma ‘yan baya.

Leave a Reply