Allah Daya Gari Bambam, Kano Ayau Hausa

Ina da asali daga Najeriya-Gimbiyar Birtaniya

Matar Yarima Hary – dan sabon Sarkin Birtaniya – Meghan Markle ta ce binciken kiwon lafiyar mata da aka yi mata ya nuna cewa kashi 43 cikin 100 na kwayoyin halittarta ‘yar Najeriya ce.

A sabon shirinta na baya-bayan nan na Podcast da take wallafawa a Spotify mai taken ‘Archetypes’ Meghan, ta fada wa wata Ba’amurkiya yar asalin Najeriya mai suna Ziwe Fumudoh da ke gabatar da wani shirin talabijin cewa ”an yi mata gwajin ne wasu shekaru da suka gabata”.

Lokacin da Ziwe Fumudoh ta tambayeta cewa ”ke yar ina ce? sai Meghan ta ce kashi 43 cikin 100 na asalinta ‘yar Najeriya ce.

Ta ci gaba da cewa ”Zan zurfafa bincike game da wannan sakamakon gwaji, saboda duk wanda na gaya wa haka, musamman matan Najeriya sai su riƙa mamaki suna cewa kamar ya,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply