GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Ilimi da cigaban matasa zan sa a gaba- Kwankwaso

Gabanin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin sanya ilimi da ci gaban matasa a gaba idan ya ci zaɓe.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamna na jam’iyyar NNPP na jihar Kano a jiya Lahadi a Kano.
Yayin da ya ke jawabi ga dubban magoya bayansa da suka taya shi murna, Kwankwaso ya ce nan da shekarar 2023, matasa za su yi murmushi kuma za su samu damar koma wa makaranta.
“Wadanda ya kamata su yi makarantar firamare za su dawo yayin da wadanda suka wuce matakin firamare za su kasance a jami’o’in kasashen waje,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa babu wata kasa da za ta iya samun daukaka ba tare da baiwa ƴan kasarta ingantaccen ilimi ba domin su ba da gudummawar su don ci gaban kasa.
Ya yi alkawarin tabbatar da samar da isassun kuɗaɗe ga ɓangaren ilimi.
Kwankwaso ya bayyana cewa ɗumbin jama’ar da suka tarbe shi a Kano na nuni da cewa suna sha’awar samun sabon tsarin shugabanci a Najeriya.
Ɗan takarar ya ce jam’iyyar NNPP ta shirya tsaf domin lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023 da manyan jam’iyyun siyasa a Nijeriya.
“Wannan taron jama’a yana nuna bukata da kuma neman sabon shugabanci ba a jihar kadai ba, har ma da kasa baki daya.
“Babban abin mamaki zai zo lokacin da jam’iyyar mu, NNPP za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023 in Allah ya yarda,” ya kara da cewa kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.

Leave a Reply