Kano Ayau Hausa, Siyasa

Idan APC ta fadi zaben 2023 ba laifina ba ne – Abdullahi Adamu

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu ya buƙaci ƴaƴan jam’iyyar su zage dantse domin nasarar jam’iyyar a 2023. Ya ce kada wanda ya ga laifinsa idan APC ta faɗi a 2023.

Shugaban jam’iyyar yace masu ƙumbar susa a jam’iyyar su sauka ƙasa su taimakawa ƙananan yan jam’iyya domin kada a fafe gora ranar tafiya.

Shafin SIYASARMU ya ruwaito cewa, Malam Adam ya yiwa ahalin APC wannan kashedi ne lokacin da ya kafa kwamitin mutum takwas da zasu sasanta ƴaƴan jam’iyyar na jihar Abia.

Leave a Reply