HANTSI, Kano Ayau Hausa

Gwamnatin Tarayya ta nada wanda EFCC ke bincika sabon Akanta-Janar na riko

Gwamnatin tarayya, ta amince da naɗin Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku a matsayin mai kula da ofishin Akanta Janar na Tarayya, biyo bayan binciken da hukumar EFCC ke yi wa dakataccen Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris, bisa zarginsa da almundahanar kuɗaɗe.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 20 ga watan Mayu, mai ɗauke da sa hannun Aliyu Ahmed, Babban Sakataren ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare ta Ƙasa.
A wannan matsayi dai ana sa ran Anamekwe zai gudanar da aikinsa bisa bin dokoki da ƙa’idoji, bisa kuma nuna cikakkiyar ƙwarewarsa.
Anamekwe ya samu sahidar karatu ta HND a fannin aikin akanta da ya karanta a jami’ar IMT da take a birnin Enugu tare da shaidar digiri na biyu a fannin sarrafa kuɗi da ya karanta a jami’ar Common Wealth da ke Belize.
Ya fara aikin gwagwarmaya da Cibiyar Nazarin Dimokuraɗiyya, CDS kuma ya kai matsayin Babban Akanta tsakanin 1992 zuwa 1995.
Anamekwe, wanda ya halarci kwasa-kwasan gudanarwa da dama a gida da waje, kuma mamba ne a ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Najeriya ICAN, sannan kuma ɗan ƙungiyar ƙwararrun masana tattara kuɗaɗen haraji ne watau CITN, kuma mamba a cibiyar harkokin gudanarwa ta Najeriya NIM.

Leave a Reply