BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Gwamnatin Tarayya ta bukaci jama’ su hada wa wadanda harin jirgin kasa ya shafa su yi jinya

Gwmnatin tarayya ta bayyana cewa ya kamata talakawa su tarawa yan uwan su kudi da harin jirgin kasa ya shafa domin a musu Magani.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce hukumar sojin kasa ta baiwa marasa lafiyan kulawa a asibitinta ba tare da ta karbi ko kwabo ba Sai dai ya ce wasu daga cikin marasa lafiyan na bukatar magunguna wadanda ba a kasar nan ake yin su ba.

Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya bukaci yan Najeriya da su kawo gudunmawar kudi domin kula da wadanda harin jirgin kasa na ranar Litinin ya ritsa da su, kamar yadda muka ruwaito daga Rariya.

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da yan bindiga suka far ma jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Amaechi, wanda ya ziyarci wajen harin a ranar Talata, ya ce ba don an toshe sayan manyan kamarori da na’urori na layin dogo da kudinsu ya kai naira biliyan 3 ba, da an dakile harin, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce kayan zai kawar da duk wani bakin wuri a kan hanyoyin jiragen kasa a fadin kasar.

Leave a Reply