Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadun.
Kawo yanzu dai ba a san abin da mutanen biyu suka tattauna ba, sai dai wasu na ganin ganawar ba ta rasa nasaba da rikicin masarautu da ake yi a Kanon.
A ƙarshen makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan Kano, Comr. Aminu Abdulsalam ya zargi Nuhu Ribadun da kitsa komawar sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero zuwa birnin, kwana biyu bayan da gwamnan jihar ya sanar da tuɓe shi daga sarauta.
Sai dai ofishin Ribadun ya musanta zargin tare da barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu idan bai janye kalaman nasa ba.