Kano Ayau Hausa, Siyasa

Gwamnan Adamawa ya dauki mataimakiya mace

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya dauki shugabar jami’ar jihar da ke Mubi, a matsayin wacce za ta yi masa mataimakin gwamna a zaɓukan 2023 da ke tafe.

Gwamnan ya ce ya dauki Matar ne, saboda kudurinsa na ganin an dama da mata a harkokin gudanarwa a jihar la’akari da irin gudunmawar da ta bayar wajen ciyar da ilimi.

Jam’iyyar PDP a jihar Adamawa ta ce ta zabi Farfesa Kelatapawa Farauta a matsayin wadda za ta yiwa gwamnan jihar takarar mataimaki a zaben 2023 ne kasancewar yana cikin kudirin su na tafiya da mata da matasa a harkokin siyasar jihar kamar yadda BBC ta kalato.

Tun lokacin da jam’iyyar APC ta tsayar da Sanata Aisha Binani don yiwa jam’iyyar takarar gwamna a jihar, ake ganin take-taken jam’iyyar PDP na cewa za ta tsayar da mace a takarar mataimakin gwamna.

A yanzu dai an zuba ido domin ganin yadda za ta kaya tsakanin jam’iyyar ta PDP da kuma APC a jihar ta Adamawa wacce ake ganin siyasar jihar ke zafi a duk lokacin da aka kada gangar siyasa a Najeriya.

Leave a Reply