Kano Ayau Hausa, Siyasa

Goodluck Jonathan ya koma APC, ya saya fom din takarar Shugaban Kasa

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ƙungiyoyin arewacin ƙasar sun haɗa hannu inda suka saya wa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan fom din takarar shugabancin ƙasar

Duk da cewa Jonathan ba ɗan Jam’iyyar APC bane, amma ana ta ce-ce-ku-ce a kwanakin baya kan cewa yana daf da sauya sheƙa daga PDP ya koma APC kamar yadda BBC ta kalato.

A 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Jonathan a zaben ƙasar, amma tun bayan nan Jonathan ya ci gaba da gudanar da ayyukan ƙungiyar ECOWAS inda ya rinƙa zuwa sasanci a wasu ƙasashen Afrika.

Leave a Reply