BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ganduje ya hana harkokin siyasa a lokacin sallar idi da bukukuwan Sallah

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya haramta liƙa hotuna da ɗaga tutocin siyasa a yayin bukukuwan ƙaramar Sallah.

Hakan na cikin saƙon sallah da Gwamnan ya fitar, ta hannun Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba.
Ganduje ya ce, daga yanzu an hana sanya tutoci, ko allunan ƴan siyasa yayin sallar idi da sauran taruka na bukukuwan sallah domin kaucewa rikici.

Ya ce, Sallar idi ibada ce muhimmiya bayan azumin Ramadana da ake bin bayanta da bukukuwan bajakolin tarihi da al’adu, wanda ake zuwa kallo har daga ƙasashen ƙetare.

Saboda haka a cewar sa bai kamata a mayar da waɗannan wurare wajen gangamin siyasa da yaƙin neman zaɓe ba.

Dr Abdullahi Umar Gandujeya jaddada cewa, ɗaga allunan siyasa a yayin taron da ya haɗa jama’a masu mabanbantan ra’ayi kamar Hawan Daushe, ka iya haifar da tarzoma.

Sanarwar ta kuma umarci ƴan siyasa da su tabbatar sun yi biyayya sau da ƙafa ga sabuwar dokar zaɓe.

Gwamna Ganduje ya taya al’ummar musulmi murnar bikin Sallah, tare da fatan za su yi riƙo da abin da suka koya a watan azumi, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Haka ma ya yi kira ga jami’an tsaro su nuna halin ba sani ba sabo, ga duk wanda yayi ƙoƙarin tayar da tarzoma yayin bukukuwan sallar.

Leave a Reply