BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

EFCC ta kama Akanta Janar na ƙasa bisa zargin sace biliyan 80

Labarai daga Najeriya suna bayyana yadda Hokumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriyar (EFCC) ta cafke Akanta Janar na ƙasa, wato Alhaji Ahmed Idris a bisa zargin badaƙalar wasu mazajen kuɗaɗe kimamin miliyan dubu tamanin.

Majiyar TDR Hausa ta bayyana cewa hukumar ta daɗe tana gayyatar Akantan don ya yi bayani, amma ya ƙi hallara a gabanta domin ya yi bayani game da tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Leave a Reply