Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Dan fim a Tunisia ya nemi a sauya lokacin Azumi zuwa hunturu

Wani fitaccen dan fim a Tunisia Mohamed Al-Siyari ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman a Gabas Ta Tsakiya bayan ya yi kiran a dawo da yin azumi lokain hunturu duk shekara.

Ya yi wannan tsokacin ne a wata tashar rediyo ta Shams FM a Tunisia a ranar Juma’a.

A tattaunawar, ya ce ya kamata “Ramadan a mayar da shi watan Disamba duk shekara, saboda azumi lokacin bazara akwai wahala,” yana kuma mai cewa “mayar da yin azumi lokacin hunturu zai ƙarfafa wa mutane yin azumi. “

Ya jaddada ra’ayinsa da cewa “addini mai sauƙi ne ba wahala ba” tare da yin tambayar cewa: “Me ya sa wai muke azumi cikin tsananin zafi?”

Ramadan wata ne na tara a kalandar Islama, kuma wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci.

Amma al-Siyari ya ce ya kamata malaman addini su haɗu su sauya lokacin azumi ya zama kamar lokaci guda da ake Kirsimeti a ƙarshen shekara.

Kalamansa sun haifar da caccaka da zazzafar muhawara a kafofin sada zumunta musamman a Tunisia da sauran ƙasashen Gabas Ta Tsakiya.

Ya kuma sake fitowa a wata tashar Rediyo ta “Mosaic FM” yana kare kalamansa cewa yana da ƴancin ya bayyana ra’ayinsa tare da ƙin amincewa ya fito ya janye kalamansa da kuma neman afuwar Musulmi kan abin da ya faɗa,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Yawancin waɗanda suka yi tsokaci a kafafen sada zumunta sun caccaki kalaman Al-Sayyari ne, wasunsu sun ce rashin ilimin addini ne ya sa har ɗan fim din ya furta kalaman.

Leave a Reply