Kano Ayau Hausa, Labarai

Da mu za a yi zaben 2023-IPOB

Ƙungiyar ‘yan awaren IPOB masu fafutikar kafa ƙasar Biafra da ke kudu maso gabashin Najeriya, ta ce ba ta da niyyar ƙaurace wa zaɓen ƙasar da za a gudanar cikin watannin Fabrairu da Maris na wannan shekara

A watan da ya gabata ne Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta a ƙasar INEC ta yi gargaɗin cewar yawan hare-hare kan ofisoshinta da ke yankin da ƙungiyar IPOB ke gudanar da ayyukansu, zai shafi shirye-shiryen hukumar game da babban zaɓen a yankin.

To amma mai magana da yawun ƙungiyar Emma Powerful ya zargi wasu ‘yan siyasa da haddasa fargaba a zukatan al’umma domin su samu damar murɗe zaɓen tare da ɗora laifin kan ƙungiyar tasu ta IPOB, kamar yadda BBC ta ruwaito.

A watan da ya gabata ƙungiyar ta yi Allah-wadai da rigingimun da ake samu a yankin kudu maso gabashin ƙasar, inda ta umarci mazauna yankin da su yi rajistar zaɓe.

Leave a Reply