Kananan Labarai

Burina in fi kowa iya zanen mota – Salim

Wani saurayi dan shekara 13, mai suna Salim Muhammad Ahmad Argungu ya ce yana da burin zama wanda ya fi iya zana mota a duniya.

Saurayin wanda ke aji biyu a qaramar sakandare ya ce ya fara harkar zanen mota ce tun yana dan shekara biyar a duniya, don yana da sha’awa.

Wannan sha’awar ta shige shi ne lokacin da sanannen mai zanen motocin nan Jelani Aliyu ya ziyarci mahaifinsa Malam Ahmad Argungu a gidansu da ke Sakkwato.

“A lokacin da Jelani Aliyu sanannen mai zana motocin nan ya ziyarce ni a gida, Salim ya fada mini cewa yana so ya zama kamar Jelani Aliyu,” inji mahaifinsa.

Salim ya fafata a gasar zana motoci na kamfanin Toyota karo na 12 (Toyota Dream Car Art) da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata. Shi kadai ne ya halarci gasar a duk Arewa ta Yamma kuma ya samu nasarar shiga cikin jerin sunayen da za a tallafa wa karatunsu don su cimma burinsu a qera motoci.

Ya samu tallafin karatu a makarantar Whiteplains British Abuja. Kuma za a tura su qasar Japan su wakilci Najeriya a wurin karatun koyon zane-zane in mutum ya samu nasara a gasar da aka yi Abuja wadda kamfanin ya shirya kuma za a gayyaci wanda ya samu nasara a bikin karbar kyauta.

“Akwai mutane da yawa amma ina da yaqinin samun nasara. Sai dai ina kira ga mawadata su taimaka mini wurin cika kudin da zan fara karatu a wannan damar da aka ba ni ta yin makarantar zane-zane da ke Abuja,” a cewar Salim.

 

Leave a Reply