Kano Ayau Hausa, Siyasa

Buhari ya umarci ministoci masu takara su yi murabus

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umarci ministocinsa masu son takara su yi murabus daga nan zuwa 16 ga watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai na ƙasar Lai Mohammed ne ya sanar wa da manema labarai hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa na mako-mako a ranar Laraba da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Daga cikin ministocin da hakan zai shafa akwai Rotimi Amaechi Ministan Sufuri da Chris Ngige Ministan Ƙwadago da Abubakar Malami Ministan Shari’a da kuma Godswill Akpabio Minsitan Ma’aikatar Harkokin Kula ds Neja-Delta.

Dukkan waɗanda ministoci sun nuna sha’awar tsayawa ko dai takarar gwamna ko ta sanata ko ta shugaban ƙasa.

Leave a Reply