Kano Ayau Hausa, Labarai

Buhari ya ba da mako biyu a kawo karshen yajin aikin ASUU

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu, mako biyu ya kawo karshen yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke yi.

Buhari ya kuma umarci Ministan Kwadago, Chris Ngige, kada ya kuskura ya halarci zaman tattaunawar sulhu da gwamnati ta kira malaman jami’ar.

Ya umarci Ministan Ilimin da ya jagoranci zaman sulhun da gwamnati ta gayyaci ASUU domin sasantawa da ita da sauran kungiyoyin jami’o’i da ke yajin aiki.

Ya ce ba wa Adamu wa’adin mako biyu ya tabbata an yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan duk matsalolin da suka hana sulhu da malaman jami’ar, sannan a kawo mishi rahoto.

Leave a Reply