Kano Ayau Hausa, Siyasa

Bayan Shekarau ya sasanta da Ganduje, Joɓe na shirin sauya sheƙa zuwa NNPP

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa,Tijjani Abdulkadir Joɓe ya yi wata ganawar sirri da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Wannan ci gaban na zuwa ne ƙasa da awanni 24 da fitar rahoton cewa jagoran G-7, wanda su ke rikici da ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya sasanta da gwamnan kuma tuni a ka yi masa alƙawarin zai ci gaba da riƙe kujerarsa ta Sanatan Kano ta Tsakiya.

Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ganawar Joɓe da Kwankwason na da nasaba da ƙoƙarin da ɗan majalisar ke yi na sauya sheƙa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP.

Wasu majiyoyin sirri sun baiyana cewa magoya bayan Joɓe ne su ka matsa lambar ya bar APC sakamakon zargin da su ka yi na cewa babu alamun Gwamna Ganduje zai yarda ya yi sulhu da Joɓen , a ƙoƙarin da ake na sulhun ta Gwamnan da ƴan G7.

Rahotannin sun tabbatar da cewa an kammala tattaunawar kuma shi Joɓen ya aminta zai koma jam’iyyar NNPP a kowanne lokaci da ga yanzu, inda kuma aka shirya yin gagarumin biki na karɓar ɗan majalisar zuwa NNPP.

Wannan ya nuna cewa gungun ƴan G-7 ɗin ya tasamma wargaje wa duba da yadda jagoran tafiyar ya bada kai bori ya hau, shi kuma Joɓe ya kama tashi hanyar.

Yanzu dai abin jira a gani shine hanya makomar Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin da kuma Sha’aban Sharada, ɗan majalisa mai wakiltar Ka ta Tsakiya a majalisar wakilai kuma ɗan takarar gwamna a jihar.

Leave a Reply