Barista Audu Bulama Bukarti da ke zaune a Landan ya sanar da kudurinsa na tallafa wa daliban Jami’ar BUK da Naira miliyan 1.
Ya sanar a shafinsa na Facebook cewa:
Tallafin Kuɗin Rejistireshin Ɗaliban BUK 20
In shaa Allah, zan tallafawa Ɗaliban BUK guda 20 da N50,000 kowanne. Za mu bawa Ɗaliban Law 5, Ɗaliban Medicine/Nursing 5, Ɗalibai masu bukata ta musamman 5. Sauran 5 ɗin kuma duk mai buƙata zai iya nema. Ma su buƙatar wannan tallafi sai su je gurin Nasiru Zango a Freedom Radio ranar Laraba domin a tantance su. Ana buƙatar kowa ya je da cikkakun takardun sheda.
Manufar wannan tallafi shine mu taimakawa waɗanda ba su da cikekken ƙudin rijistireshin. Saboda haka, don Allah idan ka/ki na da hanyar biyan rijistireshin, kada ka/ki nemi wannan. Ina kira ga duk waɗanda su ke da dan dama-dama, su ma su taimakawa adadin da za su iya da abinda ya sauwaka.
Wannan karin kuɗin rijistireshin da aka yi zai sa karatu ya gagari ‘ya’yan talaka da dama indai ba a tallafa musu ba. Allah Ya sa mu dace.