WASANNI

Barcelona ta fara zawarcin Firmino

Kulob din FC Barcelona na Sifen ya fara zawarcin dan kwallon gaba na kulob din Liberpool na Ingila, Roberto Firmino.  Kulob din ya ce ya fara zawarcin dan kwallon ne don ya gaji Luis Suarez da ya fara tsufa.

Luis Suarez, wanda zai cika shekara 32 a watan Janairun badi, yana shan suka daga magoya bayan kulob din ganin yadda kawo yanzu ya zura kwallaye biyu ne kacal daga cikin wasanni bakwai da ya buga wa kulob din a kakar wasa ta bana.

Kwantaragin Suarez za ta kare ne a Barcelona a shekarar 2021 yayin da kwantaragin Firmino kuma za ta kare ne a kulob din Liberpool a shekarar 2023.

Rahoto ya ce ba karamin kudi FC Barcelona za ta taya Firmino kafin kulob din Liberpool ya amince ya rabu da dan kwallon a wannan lokaci da tauraruwarsa ke haskakawa.

Leave a Reply