Gwarzon dan wasan gasar kofin duniya da aka kammala a Qatar, Lionel Messi, ya ce zai so ya cigaba da buga wa kasarsa Argentina wasa nan gaba.
A hira da wata jaridar cikin gida, Messi ya ce ”babu wani abu da zanyi da yafi wanda na riga na yi wa kasata, to amma zan so in cigaba da saka riga in buga wasu wasanni tare da jajirtattun yan wasan da muke dasu.”
Messi ya kara da cewa ”na matsu mu koma gida don inga irin murnar da ake yi da wannan nasara da muka samu.
A baya Lionel Messi wanda ya lashe kambun dan wasan duniya sau bakwai a tarihi ya taba ritaya, bayan gaza cin kofin nahiyar Kudancin Amurka na Copa America.
To amma kocinsu na yanzu Lionel Scaloni wanda shima tsohon dan wasan Argentina ne ya dawo dashi fagen daga, kuma sai gashi sun ci Copa America a 2021, gashi kuma sun lashe kofin duniya na Qatar 2022, kamar yadda muka kalato daga BBC.