Kano Ayau Hausa, Siyasa

Bala Muhammad ya lashe zaben gwamnan Bauchi

Hukumar INEC ta tabbatar da Bala Muhammad na jam’iyyar hamayya PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a Bauchi.

Bala Muhammad ya doke gwamna mai ci ne Muhammed Abdullahi Abubakar dan takarar jam’iyyar APC.

PDP ta lashe zaben ne da kuri’a 515,113, yayin da APC da ke mulki a jihar ta samu kuri’a 500,625

Sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa ne kadai dama ya rage, kuma PDP ce ta lashe karamar hukumar inda ta samu kuri’a 39,225, yayin da APC ta samu kuri’a 30,055.

An ta kai komo zuwa kotu bisa sakamakon karamar hukumar Tafawa Balewa musamman tsakanin hukumar INEC da kuma jam’iyyar APC a jihar ta Bauchi, bayan da jam’iyyar ta kai hukumar kotu inda ta bukaci a dakatar da tattara sakamakon Tafawa Balewa.

A ranar Talata ne dai kotun ta dakatar da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa a lokacin da hukumar ke dab da fara tattara sakamakon zaben.

Sai dai a safiyar Litinin kuma kotun tarayya da ke Abuja ta sauya matsayarta kan hukuncin da ta dauka kan dakatar da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, inda ta amince da ci gaba da tattara sakamakon zaben kamar yadda BBC ta rawaito.

Alkalin kotun ya yai watsi da batun lauyan dan takarar wato Mista Ahmed Raji, inda ya bukaci a dakatar da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa.

A hukunci da alkalin ya yanke a baya, Mista Inyan Ekwo ya ba bangarorin biyu umarnin tsayawa yadda suke har sai kotun ta yi hukuncinta.

Alkalin ya bayyana cewa karar da aka shigar a gaban kotun kara ce da ta danganci zabe kuma kotun sauraren karar zabe wato Electoral Tribunal kadai ce za ta iya yanke hukunci kan wannan batun.

Tun da farko dai Lauyan dan takarar APC ya bayyana cewa kotun sauraren karar zabe ta na sauraren kara ne kawai bayan an bayyana sakamakon zabe, a cewarsa karar da ya shigar a yanzu ta kunshi abubuwa ne da suka faru kafin bayyana sakamakon zabe.

Leave a Reply