Kano Ayau Hausa, Labarai

Babu wanda ya isa ya yi magudi a zaben 2023- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin yin magudin zabe a 2023 da su guji yin hakan, yana mai shan alwashin hana su sakat.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis da daddare yayin da ya shirya buda-baki ga jakadun kasashen waje da ke aiki a Najeriya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ta ambato Shugaba Buhari yana cewa “ya kamata wadanda suke shirin yin magudin zabe a zabuka masu zuwa su sake tunani saboda na sha alwashin kare martabar al’ummar Najeriya a yayin da suke kada kuri’unsu, kamar yadda BBC ta kalato.

Leave a Reply