BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Ba zan jagoranci Sallar Juma’a ba yau a sabon Masallaci-Nuru Khalil

Tsohon Limamin masallacin Apo Legislative Quarters da ke Abuja, Sheikh Nuru Khalid, wanda aka fi sani da Digital Imam, ba zai jagoranci sallar Juma’a a sabon masallacin da ya ce an naɗa shi limanci ba a Juma’ar yau.

A cikin bayananshi kamar yadda ya fitar a shafinsa cewa an sake ba shi limanci a wani masallaci dake Birnin tarayya Abuja.

Yayin zantawar shi da Politics Digest a ranar Alhamis, Malamin ya bayyana cewa ba zai gudanar da sallar Juma’a a sabon masallacin ba saboda wasu dalilai da suka sha ƙarfin sa.

“Malam yace saboda wasu dalilai na kashin kansa ba zai sake magana da manema labarai ba sai bayan watan Ramadan domin sanin mafaka. Wannan shawara ce da na yanke a safiyar yau kuma ba zan sassauta ba,” in ji shi.

“Zan ci gaba da yin tafsirin Ramadan a Masallacin da ke kofar gidana, a halin yanzu. Kuma zan cigaba da wa’azantarwa har izuwa kammala ibadar Ramadan”.

Idan dai za a iya tunawa, gwamitin masallacin Apo da ke rukunin gidajen ƴan majalisu a Abuja ya dakatar da Limamin daga limanci a masallacin kafin daga bisani ya tabbatar da koran shi gaba ɗaya saboda wa’azin adawa da gwamnati da ya yi kan harin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan bakwai tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Leave a Reply